Monday, February 15, 2021

Kwankwasiyya Na Karɓar Mulki Za Ta Ƙwace Kadarorin Da Ganduje Ya Siyar— Kwamared Aminu

 Kwankwasiyya Na Karɓar Mulki Za Ta Ƙwace Kadarorin Da Ganduje Ya Siyar— Kwamared Aminu 








Kwamared Aminu Abdussalam, ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano a zaɓen 2019, Kwamared Aminu Abdussalam, ya mayar da martani game da shirin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na ruse gadar sama da take Ƙofar Nasarawa.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano, ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Muhammad Garba, ta sanar da cewa za ta rushe gadar sama ta Ƙofar Nasarawa sakamakon tsagewa da ta ce ta fara yi.

Gadar saman ta Ƙofar Nasarawa dai tana daga cikin ayyukan da tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, yake tunƙaho da su.

“Abin baƙin ciki ne cewa bayan zaɓen da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Kano Ganduje a matsayin Gwamna, Gwamnan ya fara rushe abubuwan tarihi da al’ada na jihar Kano da sauran manyan gine-gine waɗanda suka ba Kano matsayinta.

“Mun ga yadda gwamnatin ta jagoranci rushe gine-ginen gwamnati masu amfani da kuma cefanar filayen gwamnati domin cin ƙazamar riba.

“Kuma muna ganin yadda Gwamnan ya rushe tare da siyar da Filin Ajiye Motoci na Shahuci, Sansanin Alhazai, Otal ɗin Daula, harabar Tashar Rediyon Kano ta Tukuntawa, Ganuwar Kano, Filin Idi na Ƙofar Mata, Masallacin Juma’a na Fage, Gidajen Malaman Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kano, harabar Gidan Buga Jaridu na Trumph da sauransu”, in ji Kwamared Aminu.

“An sani cewa a kwanan nan Gwamnan ya yi yunƙurin sauya wa Gidan Adana Namun Daji mai shekara 53 matsuguni, wanda yake da faɗin kadada 53 don siyar da shi da nufin kasuwanci.

“Bugu da ƙari, kwanan nan aka siyar da harabar Gidan Zakka, wanda ba ma na gwamnati ba ne. Wannan fa ƙari ne bisa sauran kadarori na gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane waɗanda ba za a iya ambata ba da aka ƙwace aka siyar ko aka ba iyalai, abokai da ‘yan siyasa. Saboda haka ƙarya ce tsagwaronta a ce gadar sama ta Ƙofar Nasarawa ta fara rushewa.

“A fili yake, mun ji daga majiya mai ƙarfi cewa Gwamnan yana ƙoƙarin rushe gadar saman ne don siyar da filin ga ‘yan kasuwa”, ya ƙara da haka.

Ya ci gaba da cewa: “Daga ƙarshe, irin waɗannan manufofi na ƙashin kai su suka sa al’ummar Kano suka yi fatali da APC, suka yi watsi da manufar ƙwace filaye da kuma halayyar zalunci ta gwamnatin Ganduje.

“Yayin da muke jiran sakamakon kwamitin da ake cewa an kafa, wanda tuni an tanadi sakamakonsa don biyan buƙatun kai na Gwamna Ganduje, bari in bada shawar ga gwamnati da waɗanda suke yunƙurin siyan waɗannan filaye na gwamnati cewa su kula al’ummar Kano ba za su dunƙule hannu su ga ana cefanar da kadarorin jihar ba, idan Allah Ya kai mu 2023, lokacin da Ganduje zai kammala haramtacciyar gwamnatinsa, gwamnatin Kwankwasiyya mai zuwa za ta ɗauki dukkan matakin da ya wajaba don ƙwato dukkan kadarorin da gwamnatin Ganduje ta ɓarnatar. Sun ce idan kunne ya ji jiki ya tsira”.


No comments:

Post a Comment

Pages