Saturday, February 13, 2021

Me yasa ake samun wadanda ake yada bidiyonsu na tsiraici suna lalata? Datti Assalafiy Yayi Martani Me Zafi Ga Momo

 Me yasa ake samun wadanda ake yada bidiyonsu na tsiraici suna lalata? Datti Assalafiy Yayi Martani Me Zafi Ga Momo




Datti Assalafiy yayi martani ne ga momo biyo bayan wata hira da akayi dashi a gidan rediyon freedom. A hirar momo yayi ikrarin cewa saka kudi a fim zai iya fin gina islamiyya.

Mutane da dama basu ji dadin wadannan kalamai na momo ba inda suka yi ta mayar da martani zuwa gareshi.

Shima dai shahararren marubucin nan dan gwagwarmaya a sahar facebook wato datti assalafiy yayi nashi raddin zuwa ga momo bisa kalaman da yayi. Assalafi ya nuna rashin jin dadin shi matuka da wadannan kalamai na aminu momo.

“Na saurari hiran da Freedom Rediyo Kano tayi da ‘dan Hausa film Aminu Sheriff Momo, yana cewa Zakka da Musulmai ke fitarwa ya kamata ana ware Zakkan domin shirya fina finai..” 


“Bai tsaya anan ba, Momo yace da a fitar da kudi a gina Masallatai da Islamiyyu yafi a fitar da kudin a gabatar da shirin film domin fadakarwa ne da gyara tarbiyya suke yi a film din, har yana hakikancewa.”

“Jama’ar Musulmi ku ji zance banza fa, wato lalacewar wannan ‘dan nanaye da bayyana tsantsan duhun jahilcinsa har ya kai ga cewa shirin Film ya fi Masallaci dakin Allah daraja da kuma Islamiyyah inda ake koyar da Qur’ani da Hadisi?” 




“Kullun suna cewa tarbiyya suke koyarwa a shirin film, amma me yasa ake samun ‘yan luwadi da madigo da karuwai a cikin su?”

“Me yasa ake samun wadanda ake yada bidiyonsu na tsiraici suna lalata?
Me yasa matan Hausa film suke bayyana babu hijabi tudun nonuwa da mazaunansu yana bayyana don jawo hankalin mazinata?”

Datti assalafiy ya kara da cewa babu wani abu da yan fim din suke yi face gubata tarbiyyar al’umma. Ya kara da cewa yan fim sun kasance karnukan yahudawa ne wajen gurbata tarbiyya.

“A gaskiya wadannan ba masu koyar da tarbiyya bane, muna kallon wadannan mutane ne a matsayin gurbatattun cikin mu marassa albarka karnukan farautar yahudawan duniya da akayi hayansu domin su batar da Musulmin kasar Hausa.”

“Tsakani da Allah a cikin masu harkan film ba za’a rasa mutanen kwarai ba, amma kashi 99 cikin 100 dinsu ba mutanen kirki bane, babu irin tsiya da iskanci da basa yadawa a shirin film, Masallaci da Islamiyyah ba gurin yada tsiya bane, kuma ba gurin zuwan mutanen banza bane, sun fi karfin a kwatantasu da duk wani abu mai daraja anan duniya balle shirin film dangin yahudu.”

“Muna Allah wadai da kalaman Momo, ya munana zance akan dakin Allah da inda ake karantar da addinin Allah, yayi magana kamar ya sha kwaya ko kayan maye ya bugu, tir da kalamansa akan addinin mu.

Allah wadaran naka ya lalace!”

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.

No comments:

Post a Comment

Pages