Bidiyon Boko Haram suna ganawa kan yanda zasu dauki fansar wasu manyan kwamandojin su 2 da sojojin Najeriya suka kashe
Rahotanni sun tabbata cewa Sojojin Najeriya sun kashe wasu manyan shuwagabannin Boko Haram 2, Abul-Bas da kuma Ibn Habib.
Sojojin sun kashesu ne a daidai mahadar Banki Kusa da Pulka, kamar yanda PRNigeria ta ruwaito.
Wadannan kwamandojin na bangaren shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ne kuma hakan zai matukar taba kungiyar, Kamar yanda wata majiyar tsaro ta tabbatar.
Hakanan wani bidiyo da ya bayyana Boko Haram din na ganawa akan yanda zasu dauki fansar wannan shuwagabannin nasu da aka kashe ya kara tabbatar da lamarin. Inda aka ji wani daga cikinsu na cewa kada su mika wuya.
#BreakingNews & Alert #BokoHaram #ISWAP faction admits in panic video @HQNigerianArmy @NigerianTroops have inflicted massive onslaught on Jihadist - promises to retaliate - calls on fighters to not surrender in #Local #Kanuri language. #Caution #vigilance to #Frontline troops. pic.twitter.com/skyQQhq8R2
— David Otto Endeley (@ottotgs) February 13, 2021

No comments:
Post a Comment