Bayan kwanaki 49 Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ziyarci kabarin mahaifinsa
A yammacin yau juma’a tsohon gwamnan jihar Kano kuma madugun Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyara kabarin mahaifinsa Makaman Ƙaraye hakimin Madobi, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.
Sanata Rabi’u Kwankwaso ya kai ziyarar ne jim kaɗan da saukarsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Tun da farko mataimaki na musamman ga Sanata Kwankwaso akan kafafen yaɗa labarai Saifullahi Hassan ne ya wallafa hotunan Madugun da tawagarsa a kan kabarin Makaman na Ƙaraye su na yi masa addu’a.
Idan za a iya tunawa dai a ranar 25 ga watan Disambar shekarar 2020 ne Allah ya yi wa Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya. Kuma tuni gwamanatin jihar Kano ta maye gurbinsa da Alhaji Saleh Musa Kwankwaso (Baaba)

No comments:
Post a Comment