Thursday, February 11, 2021

Asiri akaimin na aureta, nayi dana sani, cewar Usman Umar, matashin daya auri baturiya sa’ar mamanshi

 



Usman Umar, wani Mawaki dan Najeriya ya jawo ce-ce kuce a shafin Instagram bayan ya fadi halin daya tsinci kansa saboda ya auri baturiya, Lisa Hamme.

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Usman Umar, wanda akafi sani da suna Soja Boy ya bayyana yadda ya rabu da ita kuma yana godewa Allah da ya ‘yantar da shi daga hannunta. 




Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta nuna rashin jin dadinda ta da auren mace sa’arta wacce ta girmeshi da shekaru 23.

Usman ya godewa Allah kuma yace da alamun asiri tayi masa. Yace: “Ko dai an yaudarni ko kuma an yi mi asiri, kalli fuskar mahaifiyata da dan’uwana, gaba daya basu ji dadi ba amma a haka na cigaba. Na godewa mai sama da ya ‘yantar da ni.”

No comments:

Post a Comment

Pages