Thursday, February 25, 2021

Ƴan Kwankwasiyya sun baiwa mutumin nan da ya zaɓi zaman gidan yari fiye da rayuwar ƴanci jari

 

Ƙungiyar matasan Kwankwasiyya da ke unguwar Ƙaura Goje a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano wato Kwankwasiyya Consultative Youth Forum sun taimakawa mutumin nan mai suna Gambo Muhammad da tallafin jari domin fara sana’ar sayar da Kifi.


Tallafin da ƙungiyar ta Kwankwasiyya Consultative Youth Forum ta bayar ya samu ne daga hannun jagoran matasan ƙungiyar wato Alhaji Tijjani Shehu inda ya bayar da kayayyakin da ake buƙata domin fara sana’ar sayar da Kifi tare kuma da kuɗi kimanin dubu biyar (₦5000) domin sayen wani abu na gaggawa da zai ta so kuma ake da buƙata. 


Idan za a iya tunawa dai a cikin farkon watan nan na Fabrairu aka saki Gambo Muhammad daga gidan yari bayan an yi masa afuwa,sai dai ya ce ya fi son zaman gidan yari fiye da rayuwa a waje, kasancewar ba shi da wata madogara a rayuwar ƴancin.

Tun da farko an samu Gambo Mohammed da laifin kisan kai sakamakon fada da suka yi da wani a cikin shekarar 2000, kuma da fari aka yanke masa hukuncin kisa, sannan daga baya aka mayar da shi daurin rai da rai.

Gambo na daga cikin mutanen da aka yi wa afuwa a yunkurin rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya saboda ɓullar cutar korona. Ya samu ƴanci ne bayan shafe shekara 21 a gidan yari. 


Sai dai ya ce duniya ta sake yi masa zafi bayan da ya tarar mahaifinsa ya rasu, sannan an sayar da gidansu na gado. Don haka ya samu kansa a yanayin rashin inda zai zauna.

No comments:

Post a Comment

Pages