Wani Ango ya tsere aka nemeshi sama ko kasa aka rasa a ranar Aurensa wanda hakan tasa aka daurawa amaryar aure da daya daga cikin wanda suka halarci wajan bikin.
Lamarin ya farune a kauyen tarikere Taluk, dake karnataka a kasar India.
Ana tsaka da Hidimar aure Naveen ya sulale aka rasa inda yake. Saidai Thepigeonexpress ta bayyana cewa, budurwar angon ce ta masa barazanar barazanar zata je wajan daurin auren ta sha guba ta Mutu shine ya sulale daga wajan.
Wannan yasa dangin Amaryar suka tallata cewa, idan akwai wanda ke son aurenta daga cikin mahalarta bikin ya fito. Nan kuwa aka samu wani me sunan Chandrappa ya bayyana cewa yana sonta. Nan kuwa aka daura musu aure.

No comments:
Post a Comment