A wannan shekarar ta 2021 zamu gama da matsalar Boko Haram da masu satar Mutane>>Shugaba Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa a wannan shekarar ta 2021 za’a gama da matsalar Boko Haram da masu satar Mutane.
Shugaban ya bayyana hakane a masallacin Juma’a na Abuja inda aka yi addu’a dan tunawa da sojoji ‘yan Mazan Jiya. Ya nemi a saka sojojin a addu’a inda yace a wannan shekarar zasu gama abinda suka faro.
Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi ne ya wakilci shugaba Buhari a wajan addu’ar inda yace, za’a ci gaba da yiwa sojojin da suka rasa ransu wajan kare Najeriya addu’a sannan kuma za’a kula da hakkokinsu dama na wamda suke raye.

No comments:
Post a Comment