Tauraruwar Fim din Labarina da ake nunawa a tashar Talabijin ta Arewa24, Maryam Waziri aka fi sani da Laila ta bayyana dalilin da yasa take saka sarka a kafarta.
Maryam na daga cikin Taurarin Kannywood, Mata da suka je yawon shakatawa a Birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa.
A lokuta da dama akan ganta da Sarka a kafa.
Bayan da ta saka hotunanta a shafinta na Instagram wasu sun rika tambayarta dalilin da yasa take saka sarka a Kafa.
Wani ya tambayeta, Menene Amfanin wannan sarkar?
Ta bada Amsar cewa Amfaninshi Kwaliya.
Wani ma ya sake tambayarwa me yasa take yawan son saka Sarka a kafa?
Sai ta bashi amsar cewa saboda tana son ta.




No comments:
Post a Comment