- Gwamnan jihar Kano ya ajiye siyasa gefe, ya kai ziyara gidan mahaifin Kwankwaso
- Ganduje ya siffanta mahaifin Kwankwaso matsayin dattijo mai hakuri
- Ya yi alkawarin maye gurbin kujeran Makaman Karaye da wani cikin iyalinsa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar ta'aziyya wajen iyalan marigayi Makaman Karaye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.
Ganduje ya jajantawa iyalan mamacin a gidansa dake garin Kwankwaso, karamar hukumar Madobi ta jihar.
Gwamnan ya samu tarba daga kwamishanan raya karkara, Musa Ilyasu Kwankwaso, da kuma hakimin garin Kwankwaso, Alhaji Baba Musa Kwankwaso. Ganduje ya bayyana cewa: "Mun yi rashin mahaifi masu kula sosai. Allah ya jikansa kuma ya rahamshesa." Ya kara da cewa, "mahaifinmu mutumin kirki ne, mai hakuri ne, adili ne, kuma jajircacce.
Shi yasa jama'ansa ke yabonsa. Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Jannatul Fiddaus.” Yayin bada masa kan bukatar da hakimin gari, kani ga tsohon gwamna Kwankwaso, kan Ganduje ya taimaka ya bar sarautar Madakin Karaye a dangin marigayin, Ganduje ya yi alkawarin cewa "Babu bukatar wannan, saboda gidan nan ya cancanci ko ma menene daga wajenmu. Ba zamu daina girmama gidan nan ba."

No comments:
Post a Comment