Babban Limanin Masallacin Juma’a na Alfurƙan dake jihar Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar ya ce duk wanda ya saki mace a cikin shirin fim to hakan daidai yake da sakin matarsa ta gida.
Daktan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo, inda aka gan shi yana bayani game da yadda al’umma ke wasa da al’amarin saki.
A cewar Dakta Umar, duk wani ɗan wasa da ya furta wa matarsa ta fim saki, to ba bu shakka ya saki matarsa ta gida, kuma babu aure a tsakaninsu, kamar yadda jaridar Intanet mai bada labaran Kano zalla Kano Focus ta rawaito.
“Ko da wasa idan ka zo aka daura maka aure a fim, mutum ya ce ya saki matansa kuma yana da mata, kuma ya faɗa ya ce ai matan nawa duk na sake su, wai yana nufin matansa na wasan Hausa, to na gasken sun tafi.
“Ba a wasa da sha’anin saki ko kuma aure. Ka zo a cikin wasan Hausa a ce an ɗaura maka aure, san nan ka ce kuma wannan ba aure ba ne? Kuma an ɗaura aure an cika sharaɗan aure, to aure ya ɗauru”, in ji Dakta Umar.
Ya ƙara da cewa ce yawancin waɗanda ke fitowa a matsayin kafirai a cikin shirin finafinai su ma suna da gagarumar matsala ta rasa Musuluncin gaba ɗaya.

To Allah ya karemu saga sakin matanmu
ReplyDelete