Sunday, January 10, 2021

Anyi bikin taya Mansur Sokoto samun lambar girma ta mni

 Anyi bikin taya Mansur Sokoto samun lambar girma ta mni




Taron ya gudana ne a ranar Laraba 22 ga J. Akhir 1442H (06/01/2021) a babban dakin taron Makarantar Sarkin Musulmi Maccido ta hardar Alkur'ani da ke Sokoto. Kuma ya samu halartar mai girma Gwamnan Jihar Sokoto da Mataimakinsa da Wakilin Mai Alfarma Sarkin Musulmi "Wazirin Sokoto" da Sakataren Gwamnati da shugaban Ma'aikata da Manyan Malamai da Sarakuna da yan Siyasa da Ma'aikata da yan kasuwa.

A wurin taron Mai girma Gwamna ya yi kira ga Malamai da su ci gaba da hada kai da hukumomi cikin al'amurran da zasu kawo ma al'umma ci gaba. A nasa jawabin Professor Mansur ya yaba ma ayyukan da gwamnatin jihar Sokoto ta dauko na ci gaba, kuma ya yi fatar a dage domin kammala su. Haka kuma ya nemi gwamnati da ta sake nazarin samar da karin hanyoyin walwala da ba da ayyukan yi ga jama'a.



Sheikh Muhammad Isah Talatar Mafara da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Shugaban Jami'ar Usmanu Danfodiyo sun gabatar da nasihohi ga wanda aka karrama da kuma sauran al'ummar Musulmi.

Muna rokon Allah ya ci gaba da daukaka addininsa da masu taimakon addininsa, ya kawo mana zaman lafiya da wadatar arziki da ci gaba a wannan kasa.

No comments:

Post a Comment

Pages