YANZU-YANZU: Gwamnatin Tarayya Ta Umurci Ma’aikatanta Su Koma Bakin Aiki
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnatin Tarayya ta umarci ma'aikatan ta daga mataki na 14 zuwa sama, da su ci gaba da aiki a kowacce rana daga ranar Talata, 2 ga Yuni, 2020.
Shugaban ma'aikatan farar hula na tarayya, Dakta Folasade Yemi Esan ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai, Mrs Olawunmi Ogunmosunle, ta sanya wa hannu ranar Talata a Abuja.
Don haka ana umurtar duk kannin ma'aikatan gwamnatin da su koma wajan aiki, domin cigaba da aiki kamar yadda suka saba kullun; Litinin zuwa Juma’a daga karfe 9:00am zuwa karfe 2:00pm na rana a kullum.
An kuma umurci jami'an da su tabbatar sunbi dokokin wajan bin umurnin hukumomin lafiya, domin kaucewa kamuwa daga cutar Corona.

No comments:
Post a Comment