Tuesday, June 2, 2020

YANZU-YANZU: Majalisar Dokokin Tarayya Ta Amincewa Buhari Karbo Bashin Dala Biliyan 22 Daga Kasashen Waje




YANZU-YANZU: Majalisar Dokokin Tarayya Ta Amincewa Buhari Karbo Bashin Dala Biliyan 22 Daga Kasashen Waje

Daga Comr Abba Sani Pantami
Majalisar dokokin tarayya ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na ciyo bashin dala biliyan 22.7, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata bayan da ta yi la’akari da rahoton kwamitin game da yadda zaa kashe kudaden bashin.
A lokacin da ya aika da bukatar a shekarar 2019, Buhari ya ce za a yi amfani da rancen kudin ne domin a samar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin kasar.

Amma wasu 'yan majalisar musamman wadanda ke kudu maso gabas sun yi adawa da matakin, suna zargin cewa an cire yankin a cikin shirin aiwatar da kashe kudin bashin.

No comments:

Post a Comment

Pages