Ba Za Mu Bude Makarantu Ba, Har Sai Mun Tabbatar Da Babu Wata Fargaba Ta Yiwuwar Dalibai Za Su Kamu Da Cutar Corona, Cewar Gwamnatin Tarayya
Daga Comr Abba Sani Pantami
A ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar korona a kasar nan.
Hakan ya biyo bayan shawarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba daga kwamitin kar ta kwana na kasa da aka kafa kan cutar korona.
Shugaban kasar ya amince a bude wuraren Ibada; Masallatai da Majami'u kadai, da kasuwanni a fadin kasar amma da sharadin za a bi dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta.
Gwamnatin tarayya ta kuma tabbatar da cewa, har yanzu makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a yayin da adadin mutanen da cutar korona ta harba a fadin kasar suka zarta 10,000.
Ya kara da cewa, su na kokarin tabbatar da cewa ma'aikatar ilimi ta tarayya ta samar da ka'idoji da tsare-tsaren bude makarantu cikin aminci ba tare da fargaban kamuwar wani daliba ba, idan aka bude makarantun.

No comments:
Post a Comment