Thursday, April 5, 2018

Ya Boye Kananan Yara Mata Guda Hudu Yana Lalata Da Su A Jihar Kebbi





Ya Boye Kananan Yara Mata Guda Hudu Yana Lalata Da Su A Jihar Kebbi

A yau Alhamis 5/4/18 'yan kungiyar banga suka kama wani mutum mai kimanin shekaru 35 da haihuwa, inda ya boye kananan yara mata su hudu masu kimanin shekara 8 zuwa 12 yana lalata da su.

'Yan bangar sun hannantashi ga hukumar hisbah ta jihar Kebbi domin gurfanar da shi gaban kotu.

Da yake amsa tambayoyi daga jam'ian Hisba, Abdul-Aziz yar karbi laifinsa na boye kananan yara da kuma lalata da su. Ya bayyana cewar ya jima yana wannan munmunan aiki sai yau ne dubun sa ta cika.

Alhaji Abubakar Muhammad Augie Daraktan shari'a na ofishin Hisbah, wanda ya gabatar da mai laifin gaban 'yan jarida da kuma kungiyoyin mata, ya yi Allah wadai da wannan lamarin, ya bayyana cewar za su gufanar da shi gaban kotu don fuskantar shari'a.

Alhaji Suleiman Muhammad, wanda shine shugaban hukumar Hisban, ya yi kira ga uwaye mata da su guji azawa yaransu tallace-talkace domin shine tushen lalacewar 'ya'ya mata.

Mukaddashin kungiyar kare hakkin mata da kananan yara ta jihar Kebbi wato (WRAPA) Malam Nasir Idris ya bayyana cewa kungiyarsu za ta bi shari'ar a kowane mataki don ganin an hukuntar da shi yadda doka ta tanada.

No comments:

Post a Comment

Pages