Saturday, March 17, 2018

Dandalin Kannywood: Rawar Fatima Ganduje ta birge ni, da ta gayyace ni tare za mu cashe - Daso





A yayin da mutane maza da mata da kuma da musamman ma malaman addinin musulunci da dama suka yi ta suka tare da Allah-wadai da irin yadda diyar gwamnan Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje ta zazzagar da zallar farin cikin ta a lokacin bikin ta, ita kuwa jaruma Daso ta yi tsokaci kan lamarin.

Kamar dai yadda muka samu, jarumar ta shirin fina-finan Hausa watau Saratu Gidado da aka fi sani da sunan Daso ta bayyana cewa ita amaryar birge ta ma tayi domin kuwa ta nuna farin cikin ta a fili.

Tauraruwar fina-finan Hajiya Saratu Gidado haka zalika ta kara da cewa ita da ma ta gayyace ta to da duk wannan rawar da ita za'a yi ta domin kuwa ita irin wannan ranar sau daya take zo wa mutum a rayuwar sa.


Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shugaban hukumar nan ta tabbatar da da'a tare da dabbaka tarbiyya a jihar Kano ta Hisba watau Sheikh Malam Aminu Daurawa daga karshe ya yi tsokaci game da auren diyar Gwamnan jihar Fatima Abdullahi Ganduje da kuma angon ta Idris Ajimobi da ya gudana a jihar.


A cewar sa, a ranar Asabar jim kadan bayan kammala dauren auren ne ya tafi jihar Sokoto domin halartar bikin kaddamar da littafin Mansur Sokoto daga nan kuma ya tafi jihar Zamfara kafin kuma ya wuce Kaduna inda anan ma yayi wa'azi sai a jiya ma ya dawo.

No comments:

Post a Comment

Pages