An bukaci dukkanin mabiyan darikar Tijjaniyya dake a fadin Najeriya da su guji aikata abubuwan da zai sa mutuncin darikar ya zube a idanun mutuna da suka hada da kwadayi da kuma neman abun duniya.
Shugaban darikar ne dai na jihar Jigawa tare kuma da wakilin babban jagoran darikar Umarul Futi ya bayyana hakan a garin 'Yanlleman a jihar Jigawa a yayin babban gangamin taron maulidin da aka gudanar. Hausazone.com dai ta samu cewa shugabannin na darikar dai sun yi wannan kiran ne biyo bayan irin yadda zarge-zarge suka yi yawa a tsakanin al'umma na ganin yadda darikar ke neman ta koma kamar ta neman kudi a hannun wasu 'yan tsiraru.
A cewar shugabannin darikar ta su ta ginu ne a bisa kan tafarkin al'qurani da sunna sannan kuma a kan cikakkiyar koyarwa ta jagoran su Ahmadu Tijjani.
No comments:
Post a Comment