Monday, December 11, 2017

Sharhin Film din kisan Hutu

Tare Da: Saddika Habib Abba
Suna: Kisan Hutu
Tsara labari: Yakubu M Kumo
Furodusa: Nazir Auwal (Dan Hajiya)
Bada umarni: Mal. Aminu Saira
Kamfani: Dan Hajiya Film Production
Jarumai: Ali Nuhu, Jamila Umar Nagudu, Tijjani Faraga, Ahmad Ali Nuhu, Ahmad Ilyasu Abdulmuminu da sauran su.
Kisan hutu a farkon labarin an nuna yan da Nabil (Ahmad Ali Nuhu) yake tsananin nu na kiyayya ga mahaifinsa Ahmad (Ali Nuhu) Nabil yana zaune da kowa lafiya yana kaunar mahaifiyarsa Zainab (Jamila Umar Nagudu) yana kaunar kowa amma shi mahaifinsa ne kawai ba ya so, ko kusa dashi yazo sai ya ta shi ko muryarsa ya jiyo bazai do so wurin ba, ko taba shi yayi tamkar ya zuba masa wuta sai ya fizge hannun, abin yana matukar da mun Zainab mahaifiyar Nabil kullum acikin da muwa take da kukan wannan kiyayya da Nabil yake gwadawa mahaifin na sa duk da irin tsananin soyyayar da shi mahaifin na Nabil yake nu na masa
Mahaifiyar Nabil ta ce ko’a lokacin da Nabil yana jariri mahaifin na sa ko taba shi yayi sai ya saka gigitaccen ihu ko bacci yake yi kuwa ballantana kuma ga idan ya daukeshi, haka rayuwarsu takasance har girman Nabil tun abin ba ya da mun mahaifin Nabil sosai yana iya daurewa yana cewa kuruciya ce har ta kai ga ya sa re, domin akwai lokacin ma da mahaifin na sa ya rike shi yaki sakinsa tsananin kiyayya ta saka Nabil ya yi wa mahaifin na sa kashe din idan har bai sake shi ba sai ya kashe shi, wannan furucin na Nabil ya yi matukar gigi ta mahaifin Nabil shine abinda ya daga wa mahaifiyar Nabil hankali ita ma ta sa ke koma wa wurin Malamin da take zuwa yana yi mata bincike akan matsalar Nabil, tana zuwa wurin Malam (Kabiru Nakwango) tayi masa baya nin duk matsalar Nabil da mahaifin sa, shi kan sa Malamin abin ya yi matukar gigi ta shi domin ya ce bai taba jin irin matsalar Nabil ba a rayuwarsa. a lokacin ganin damuwar data ke ciki tasan ya Malam ya yi mata nasiha sannan ya kawo addu’oi ya ba ta kuma ya umarce ta data zo masa da mahaifin Nabil akwai tambayoyin da zai yi masa.
Bayan ta da wo gida ta sanarwa da mahaifin Nabil abinda Malam yace amma yaki yarda da ita sakamakon boko data ratsa shi, domin likita ne babba a kasar waje ma ya yi karatunsa har yana da asibitin sa na kan sa wannan dalilin ne ya sanya ya ki amincewa da ita kai tsaye, domin ya ce matsalar Nabil a kwakwalwarsa ta ke kasar waje zai kai shi ayi masa magani matsalar ta asibiti ce ba ta malamai ba.
Zainab ta koma ta sanarwa da Malam har ta tafi masa da Nabil a lokacin Malam ya yi wa Nabil tambayar meyasa ba ya son mahaifin sa? Nabil yake ce masa saboda yana bin magan ganun shaidan, a wannan furucin da Nabil ya yi Malam ya fuskanci akwai wani abu a boyayye sannan ya sake umar tar Zainab duk yan da za’ayi ta turo masa Ahmad, bayan Zainab da Nabil sun taho hanya Zainab ta sa ke tambayarsa meyasa yake yiwa mahaifin sa haka? anan ne Nabil yake shaida mata bashi kadai yake kin sa ba domin ubangiji ma yana fushi dashi Zainab ta tambayeshi waya fadamasa Nabil yace mata wani tsoho ne yake fada masa a mafarki.
Sai da tura takai bango Ahmad ya tafi wurin Malamin da Zainab take zuwa Malam yayi masa tambayoyi akan ba shida matsala da ko wa? Ahmad yace masa ba shida ita amma duk san da ya kwanta bacci yana yin mu gayen mafarkai da mahaifin sa, Malam ya sa ke tambayarsa shin sun rabu da mahaifin sa lafiya? Ahmad yace masa e, domin har ya mutu yana saka masa albarka, Malam ya umarci Ahmad akan yaje ya yi tinani bayan Ahmad ya da wo gida ya fadada tinanin sa sai ya tino wani abu sai ya koma wurin Malam ya fadamishi cewa tin yana karami mahaifiyarsa ta rasu mahaifin sa shine yadauke duk dawainiyarsa yana tsananin kaunarsa ya fada wa malam duk sha kuwarsu da mahaifinsa har bayan ya girma ya tafi kasar waje karatun likita, bayan ya gama ya dawo mahaifin sa ya fadi jinya ya kwantarda shi a asibitin sa har ta kai ga jikin mahaifin na sa ya yi tsanani har ya shiga ‘koma’ yana raye amma kuma tamkar yana mace shi kuma saboda kaunar da yake yiwa mahaifin na sa saboda yasan irin azabar da yake ji kuma ya tabbatar bazai ra yuba hakan ya sanya yayi abinda yaga turawa suna yi wato “Kisan hutu” a lokacin ya yi masa allurar mutuwa saboda yasami rangwamen jin ya da aza bar da yake ciki domin shi aganin sa hakan da ya yi soyyaya ya gwada wa mahaifin na sa.
Bayan Ahmad ya gama bai wa Malam labari Malam ya tabbar masa da cewar kisan da ya yi wa mahaifin sa dai dai yake da ya dauki wuka ya daba masa Malam ya fito wa Ahmad kuskurensa sosai ya nuna masa cewar karancin ilimin addini shine ya san ya ya dauki dabi’ar yahudanci Malam ya jan yo a ya ya fassara wa Ahmad akan illar abinda ya yi sannan ya ba shi shawarar yaje ya ne mi ga farar ubangiji. bayan Ahmad ya da wo gida abin ya da me shi sosai har ta kai ga ya dauki allurar mutuwa shima zai yi wa kan sa matarsa Zainab ta hana shi dakyar daga nan Ahmad ya yi nadamar abinda ya aikata ya durfa fi istigfari a lokacin ya sami afuwa daga wurin dansa Nabil har ya fara kunarsa ya fa ra damuwa dashi.
Abubuwan birgewa:
1-Sunan fim din ya hau da labarin sosai.
2- An yi amfani da kayan aiki ma su kyau a wurin guda nar da fim din musamman camera ta daukar hoto da kuma abin daukar sauti.
3- Mai ba da umarnin fim din ya yi kokari wurin fassara labarin daga rubutu zuwa hoto mai motsi.
4- An yi amfani da sutturu ma su kyau wanda suka da ce da labarin
5- Akwai darasi sosai acikin labarin musamman yan da aka fito da illar sa ba wa iyaye.
Kurakurai:
1- Akwai in da Ahmad yana karami yake fada wa mahaifin sa an ce aka wo kudin makaranta kuma kayan makarantar Ahmad an nuna kaya ne irin na makarantar gwamnati ai kowa yasan makarantar gwamnati a can can shekaru na baya ba’a biyan kudin makaranta tinda tarihin rayuwar Ahmad ta kuruciya ake nu na wa, duka duka makarantar gwamnati a wannan ‘yan shekarun aka fara biyan kudi amma ba’a shekaru dayawa kamar yan da aka nuna kuruciyar Ahmad ba.
2- An nuna Ahmad yana rayuwa da mahaifinsa yana karami kuma kwatsam mai kallo sai yaga Ahmad an nuna ya dawo daga kasar waje karatu ya je har kasa biyu Amurka da Jamani ba’a ga sanadin tafiyar Ahmad ba ba’a ga waye ya kaishi ba, tinda yanda aka nuna mahaifin Ahmad talaka ne bazai iya biya masa yaje har kasa biyu ya yi karatu ba, shin wanene ya kai Ahmad kasar waje? idan ma gwamnati ce ya kamata ace an fada ko da a baki ne.
3-An nuna mahaifin Ahmad babu abinda ya can ja a tare dashi na manyanta tun Ahmad yana karami har tsahon shekara sha bakwai yana nan a yan da yake.
4-Akwai in da Zainab take fadawa Malam tun bayan kammala karatun Ahmad na sakandire ya sami gurbin aiki a kasar waje yaje yayi karatu a kasar wajen, shin wanne mai kallo zai dauka? gurbin aikin data ce ya samu ko kuma gurbin karatun? kamata yayi Zainab tace Ahmad ya sa mi gurbi na karatu a kasar waje bayan ya kammala ya sa mi aiki.
5- Akwai in da Ahmad yake fadawa Zainab za ta raka shi wurin Malam amma kawai sai aka ga Ahmad shi kadai ba bu zainab din a wurin malam, shin ya akayi yazo babu ita tinda ita kadai tasan wurin domin rako shi dama za tayi.
6- A lokacin da mahaifiyar Ahmad za ta rasu mai kallo yaga tana yi masa wani irin kallo har Ahmad yake ce mata meyasa kike kallona? ya kamata ace an fassara wa mai kallo wannan kallon da ta ke masa, ko da ma ta san abinda zai aikata a gaba shiyasa take kallonsa?
7- Akwai in da Ahmad yake fadawa malam shi bazai iya tuna rayuwarsa da yayi da mahaifiyarsa ba domin lokacin data mutu yana karami, a yanda aka nuna shekarun Ahmad da lokacin da mahaifiyar ta sa ta mutu girmansa da wayonsa bazai yu wu ace bazai iya tina rayuwar da yayi da ita ba.
8- Shin Ahmad da Zainab basu da dangi ne ? har aka gama fim din ba’aga wani dan uwansu ko daya ba wanda matsalar da suke ciki kamata ya yi ace an nuna wani ko da acikin ‘yan uwan Zainab ne wanda yake taya su jima mi da kuma shawarwari.
9- A lokacin da aka nuna mahaifiyar Ahmad ta rasu a shekarun Ahmad da wayonsa bazai yu ace baisan mutuwa ba, ya kamata ace an ganshi yana kuka ko kuma an ganshi acikin damuwa amma idonsa kamas ko damuwa ba’a gani a fuskarsa ba.
10- Akwai in da Ahmad yake nuna wa Zainab zargin ko ba shine mahaifin Nabil ba? Nabil yana kwance yana bacci lakadan kawai sai akaji yana magana yana bai wa mahaifin na sa amsar cewa shi dansa ne kuma da jininsa aka halicce shi, duk wanda yake bacci bai san abinda yake faruwa ba ballanta har yayi magana muhimmiya irin wannan kuma ba magagi ba, kuma akaga Nabil ba farkawa yayi ba yana ci gaba da baccin, shin waya fadawa Nabil wannan amsar har ya fade ta yana bacci? idan mahaifin Ahmad ne ya fadamasa kowa yasan wanda ya mutu baya dawo wa, wannan maganar da Nabil yayi kamata yayi ace a farke ya fadawa mahaifin na sa ba’a bacci ba domin hakan da’aka nuna ba duk masu kallo bane za su gamsu da hakan ba.
Karkarewa:
Fim din ya yi kyau sosai kuma an yi amfani da salo na rike hankalin mai kallo har a gama bai gaji ba, amma kuma an takaita abubuwa da ya wa wanda ya kamata abuda su. Allahu a’alamu.

No comments:

Post a Comment

Pages