Daga cikin 'yan takarar da zasu fafata a neman shugabancin jam'iyyar a gobe sun hada da; Uche Secondus, Cif Gbenga Daniel, Jimi Agbaje, Sanata Rasheed Ladoja, Farfesa Taoheed Adedoja, Farfesa Tunde Adeniran, Cif Olabode George, Dakta Raymond Dokpesi, da kuma Mista Aderemi Olusegun.
Shugaban kwamitin taron kuma kayayyen dan takarar gwamnan Jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu, ya damka takardar sahalewar tsayawa takarar ga dukkanin mutanen. Ize-Iyamu ya ce jam'iyyar zata lika sunayen ragowar masu neman mukamai da aka tantance a sakatariyar jam'iyyar. Gabanin taron gangamin, Jam'iyyar PDP, ta gargadi masu son yin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar da su guji mayar da taron dandalin yakin neman zabe.
No comments:
Post a Comment