Wednesday, December 27, 2017

Miji Da Mata Sun Shiga Hannun Hukuma Bisa Kona Al'urar Dansu Saboda wannan dalilin


Mista Ayo da matarsa Khadija sun shiga hannun hukumar yaki da fataucin yara ne bayan zargin Khadija da kona hannaye da al'aurar yaron mai shekara biyu wanda dan kishiyarta ne.
Rahotanni sun nuna cewa, lamarin wanda ya auku a garin Kuje dake Abuja a cikin makon da ya gabata, bincike ya nuna cewa tun bayan da aka saki mahaifiyar yaron ya koma karkashin kulawar kishiyar uwarta sa, ba ya samun wadataccen abinci, wanda hakan ya sa a wasu lokutan yakan dauki abinci idan an ajiye ya ci koda ba a umarce shi da hakan ba.
Inda a wannan karo bayan yaron ya ji yunwa, sai ya dauki alalan da kishiyar mahaifiyar tasa ta dafa ya ci, wanda hakan ya jawo aka yi masa wannan hukuncin.

No comments:

Post a Comment

Pages