Monday, December 11, 2017

Fim Din Sarauniya Ya Tayar Da Kura A Wajen ‘Yan Fim




Fim Din Sarauniya Ya Tayar Da Kura A Wajen ‘Yan Fim



A ’yan kwanakin nan duk inda ka shiga a cikin masa’antar finafinai ta Kannywood babu abinda za ka ji a na yi sai takaddamar da fim din Sarauniya wanda kamfanin Rite Time Multimedia ya shirya kuma a ka yi bikin kaddamar da shi a karshen watan da ya gabata.
Koda ya ke tun daga lokacin da a ka fara shirye-shiryen fara aikin a ka fara tsokaci a kansa, musamman irin sabon salon da a ka zo da shi, wanda ba a saba yin sa ba a masa’antar finafinan ta Hausa. Domin kuwa an yi ma sa tsari ne irin yadda a ke yin tsarin aikin finafinai a duniya, inda a ka shafe tsawon kwanaki a na tantance jarumai mata sama da guda 50, inda a cikionsu ne a ka zabi jaruma Asabe Madaki domin ta fito a matsayin jarumar fim din.
Ita kanta Asabe Madaki yin nasarar ta a wajen tantancewar ya bada mamaki, domin kuwa akwai manyan jarumai na Kannywood da su ka shiga gasar, amma ba su kai ga nasara ba. Sai ita da a ke ganin ta a matsayin bakuwar fuska.
Hakan ya cire tunanin da wasu su ke yi na cewa ana yin son rai wajen zabar jaruman da su ke taka rawa a finafinan Hausa. Idan ma dai ana yi to a fim din Sarauniya ba a yi hakan ba, domin an bi cancanta ne kawai. Sannan a bangaren jaruman da suka fito a fim din shi kansa wata sabuwar magana ya haifar, domin kuwa an dade ba a yi wani fim da ya tara manyan jarumai na Kannywood kamar fim din Sarauniya ba.
Don kuwa duk wani jarumi da ya amsa sunansa kuma a ke ji da shi a Kannywood, to ya fito a cikin fim din. Wannan ta sa tunda a ka fara aikin fim din a gidan Sarkin Dutse na Garu da ke Jihar Jigawa, jama’a daga garin Kano zuwa sauran jihohi su ka rika uwa domin ganin yadda aikin fim din ya ke tafiya. Don haka wajen ya zama kamar wani wajen yawon bude ido. Saboda irin cikar da wajen yake yi un daga safe zuwa dare.
Alhaji sani Sule Katsina shi ne shugaban Kamfanin Rite Time wanda yake shirya wannan fim din. Mun tambaye shi yadda ya samar da wannan labarin fim din da kuma manufar sa a game da fim din, inda ya ke cewa, “to, shi wannan labarin an zo min da shi ne daga baya, amma tunda farko ina so ne a rubuta min labarin fim wanda zai zama daidai da labarin Sarautar mu ta Afirka, kuma ya zamo mai ingancin da zai yi gogayya da duk wani fim da ake ji da shi a Afirka. Don haka ne na samo Ibrahim Birniwa don ya samar min da labarin. To a lokacin shi ya ce yana da labarin, kuma mai karfi har ya kai wa wasu manyan furodusoshi amma suka ce aikin zai ci kudi da yawa. To da ya kawo min na duba kuma na bai wa kwararru suka yi nazari suka tabbatar min da ingancin labarin, sai na amince muka daidaita shi ne na fara aikin.”
Mun tambaye shi a game da maganar da ake yadawa na cewar, fim din zai ci Naira Miliyan 20 wajen gudanar da iakinsa. Ko haka abin ya ke? Sai ya ce, “maganar zai ci miliyan 20 ba shi ba ne abin dubawa, mu manufarmu ita ce mu yi abu mai kyau da inganci. A yau mu na bukatar manyan finafinai masu inganci wanda za mu yi alfahari da shi a duniya. Idan har a ka ce fim din Sarauniya ya kai ga wannan matsayi to ko miliyan dari na kashe ni abin alfahari ne a gareni.”
A kan yadda fim din ya kunshi jarumai masu yawa kuma fitattu kuwa da mu ka tambaye shi cewa ya yi, “Ba wani abu ya sa muka yi hakan ba sai don mu mu samar da fim mai inganci, don haka muka samo kwararrun jarumai wadanda suka goge. Baya ga haka ma ai mun zuba sabbin fuskoki da yawa, domin idan ka duba ita kanta jarumar da ta ja fim din ai ba fitacciya ba ce, ta cancanta ne da matsayin ake ba ta. Don haka duk wanda ka ga ni a matsayin da ake ba shi a fim din cancantarsa ce ta sa aka ba shi.”
Ko Sani Katsina ba ya tunanin yadda finafinan kasuwar fim ta ke a yanzu musamman ganin yadda ya zuba kudi masu yawa a cikin aikin sai ya ce, “to, duk da yake wannan shi ma ba zai hana ka zuba kudi mai yawa ba wajen samar wa masa’antar fim mai inganci duk da halin da kasuwa take ciki akwai hanyoyin da za mu bi wajen sayar da kayanmu ba wai sai ta hanyar sayar da fim ba a kasuwar Kofar Wambai ba. Don ka san yanzu da ka biyo muke sha ga na satar fasaha wadda kullum muke kira ga masu kallo da su daina sayen fim na satar fasaha, domin ba don masu kallo suna sayen fim na satar fasaha ba to babu wani rance da za mu nema daga wajen gwamnati sai dai Gwamnati ta zo ta yi rance a wajenmu.”
Ita ma jarumari fim din Asabe Madaki mun nemi jin ta bakinta a game da yadda ta samu kanta a fim din da kuma irin rawar da ta taka a fim cin, inda ta ba mu amsa da cewa, “Gaskiya na ji dadi sosai da na samu nasara a wajen tantancewa, wanda hakan ya ba ni damar fitowa a matsayin jarumar fim din Sarauniya. Duk da cewar, ni sabuwa ce a harkar fim din Hausa, to na yi mamakin yadda na iya rike matsayin jarumar fim din. Amma dai na san wani abu ne daga Allah. Na yi wani fim da Hausa a baya mai suna Laraba, wanda aka nuna shi a gidajen talabijin. Amma wannan ya fi burfge ni saboda ni ce jarumar kuma wannan labarin ya fi jan hankali sosai. Kuma hakan zai taimaka min na kara samun karbuwa a cikin harkar finafinan Hausa.”
Ita ma Hannatu Bashir, jarumar fim din kuma furodusa, ta bayyana mana matsayin ta a game da fim din, inda take cewa, “To gaskiya ni ina ganin fim din Sarauniya ya zama wani fitilar Kannywood a yanzu, domin idan ma an yi kamar sa to zan iya cewa an dade ba a yi fim kamarsa ba, musannan idan ka ga yawan jaruman da aka tara. Don ka san yanzu mun saba da labarin da za a yi shi a falo da cikin gida, amma shi wannan fim din labari ne da ya kunshi irin sarautarmu ta lokacin baya wanda kuma aka shiga edaji da kuma gidan sarauta domin shirya fim din. Kuma a gaskiya matakin da na taka ya burge ni, domin kusan ni ce jarumar sarauniyar, domin idan babu ni to wasu abubuwan ba za ta iya gabatarwa ba. Ni zan ce mata ki yi abu kaza don haka ni ina ganin wannan fim din ya fito da wasu darussa da dama musamman ma abin da ya shafi sarautarmu ta gargajiya.”
A yanzu dai bayan kaddamar da fim din ana jiran fitowarsa kasuwa a ga irin rawar da zai taka a tsakanin finafinan da aka yi na Kannywood musamman ma dai a yanzu da kasuwar take kokarin farfadowa daga mutuwa a lokacin baya. Saboda yanayin da ake gani a yanzu nan gaba kadan akwai fatan kasuwar za ta dawo sharafinta.

No comments:

Post a Comment

Pages