Wednesday, December 27, 2017

An Rabar Da Man Wani Gidan Man Fetur Kyauta Ga Mabukata Saboda wannan dalilin



Rundunar hadin guiwar masu ruwa da tsaki a harkar man fetur, wanda ya hada da NNPC, DPR da kuma NSCDC ta gano wani gidan mai mara lasisi wanda yake sayar da man fetur akan naira 250 a duk lita daya a Kubwa dake Abuja, inda rundunar ta rabar da man baki daya kyauta ga masu ababen hawa. Hakan ya faru ne rana ta uku a cigaba da rangadin da rundunar hadin guiwar take yi a wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara. Inda ta yi nasarar bankado gidan man fetur din mara lasisi inda yake sayar da man sama da farashin da gwamnati ta kayyade na N145 a kowace lita. Shi dai wannan gidan man da aka gano wanda yake da zamansa a Kubwa dake garin Abuja an gano cewar ba shi da lasisi, sannan kuma yana sayar da man a sama da farashin gwamnati sannan kuma a halin yanzu yana da sama da litar mai dubu sha shida a ma'adanar sa wanda ya boye ba ya sayarwa mabukata.

No comments:

Post a Comment

Pages