Wadannan abubuwan guda 10 sune zaka fara ji a jikin ka idan zuciya ta fara samun matsala:
1. Numfashi sama-sama
2. Kake jin kan ka tamkar ba nauyi
3. Rashin jurewa motsa jiki
4. Tari; matsakaici ko mai tsanani
5. Numfashin dake bayar da sauti
6. Saurin gajiya
7. Daukewar jin yunwa
8. Kumburin fuska da kafafu
9. Wahalar shakar numfashi yayin kwanciyar ruf da ciki
10. Faduwar gaba ko saurin bugawar zuciya
Masana harkar Lafiya na yawan shawartar jama'a da suke zuwa asibitoci domin yin gwaje-gwajen tabbatar da lafiyar su, ba sai sun ji basu da lafiya ba.
No comments:
Post a Comment