Ga Kurakuran kamar haka
1- A lokacin da Bashir (Aminu Sharif) ya shigo bayan mota ya zauna ku sa sosai da Na’ima ya na yin zaman da ya yi kusa- kusa sosai da Na’ima hakan ya saɓawa addinin musulinci domin ba maharraminta ba ne tunda an gina jaruman ne suna kan tafarkin addinin musulunci.
2- A yanda aka bayyana tarin dukiyar Alhaji Dan Tani a fim da irin manyan motocin da su ke gidansa da kuma yanda ya ke ji da Na’ima motar da Bashir ya kai Na’ima gidan biki sam bai ma da ce ace akwai irin wannan karamar motar ma a gidan Alhaji Ɗan Tani ba ballan ta na har a ɗauki Na’ima acikin wannan ƙaramar motar.
3- A lokacin da Na’ima ta buƙaci tana son shan alawa har ta aiki Bashir ya siyo ma ta a ƙofar gida acikin shago lokacin da Bashir ya siyo ya kawo ma ta alawar wannan ledar da aka sa ko alawar aciki leda ce irin wacce manyan kantina su ke amfani da ita amma ba shago irin na cikin unguwa kamar yanda Na’ima ta amba ta ba.
4- Acikin fim ɗin an nuna cewar Alhaji Ɗan Tani cikakken mutum ne mai hankali ba galma galma ba amma yanayin irin hirar da su keyi tare da mai gadin gidan sa Jalolo (Ado Gwanja) abun ya yi ya wa ace cikkakken mutum mai hankali ya na yin irin wannan surutan barkatai da irin wasu abubuwa da Alhaji ya din ga gudanar wa na soyyaya tare da Na’ima a gaban ‘ya’yan sa da direban sa da mai gadin sa cikakken mutum kamar Alhaji Ɗan Tani bai da ce a ganshi a wannan yanayin ba.
5- Alhaji Ɗan Tani An nuna shi a matsayin mutum mai tarin dukiya a fim ɗin amma har fim ɗin ya kare mai kallo bai ga sana’ar da ya ke yi ba, an dai ji wataran sau ɗaya ya faɗawa Na’ima yana da taro amma ba’a faɗi kona me ne ne ba, a irin wannan tarin dukiyarsa ya kamata ace an nuna sana’ar sa ko kuma an faɗe ta.
6- Acikin wasu hotuna na fim ɗin an dabar bar tar da hankalin wasu daga cikin masu kallo ba’a buɗe abun yanda kowa zai fahimta ba domin a wani hoto anji Alhaji yana maganar ƙan ƙa rar Na’ima kuma anji wataran suma iyalan Alhaji suna maganar ƙan ƙa rar har Bashir ya na cewa zai je ya ka she firji ƙan ƙa rar ta nar ke duk abunda za’ayi sai dai ayi a gidan, har su Lami da Larai suna bashi hakuri masu kallo da ya wa basu fahimci wannan hotunan na maganar ƙan ƙa ra ba shin ƙan ƙa rar ta meye ? tunda a yanda aka nuna tana da matuƙar muhimmanci.
7- A yan da aka nuna gidansu Na’ima da irin sutturar jikin Na’ima da iyayenta talaucinsu bai kai ace har lokacin da Alhaji Ɗan Tani ya bai wa mahaifin Na’ima dubu ɗari uku ba har ya din ga kuka yana Faɗar tunda ya ke a rayuwarsa ko dubu ashirin bai ta ɓa riƙewa a matsayin ta sa ba wannan gidan da aka nuna shi a matsayin gidansu Na’ima ko ha ya suke yi yafi ƙarfin ace wanda ya ka ma wannan gidan haya bai ta ɓa riƙe dubu ashirin ta sa ba.
8- An nuna yanda Naziru yake tsananin son Na’ima har yana faɗar cewa zai iya mutuwa idan bai sa me ta ba domin tun tana shekara shida ya ke rukon ta bai kama ta ace lokaci ɗaya da Alhaji ya buɗe masa ido da kuɗi ba akan yabar ma sa Na’ima ba ace Nazir ya yi saurin amincewa ya zaɓi kuɗin ya bar Na’ima ba a irin yanda aka nuna tsananin son da ya ke yiwa Na’ima da irin ko ke ko ken da ya ke yi akanta ace farat ɗaya ya ɗabi kudi akan soyyayar ta sa ba.
9- a hoton karshe na fim ɗin an nuna Alhaji da Bashir da Raihana a wani wuri a tsai tsaye ba’a bayyanawa mai kallo ina ne wannan wurin ba sannan magan ganun da suke tattaunawa muhimmancinsu bai da ce ace an nuna su suna yi akan hanya a tsai tsaye haka ba domin magana ce wadda ya kamata a gan su acikin gida a zaune ana tattauna ta.
Ƙarƙarewa
Fim ɗin Mijin Yarinya an yi mutuƙar ƙoƙari wurin nishaɗantarwa da abubuwan ba da dariya, amma wasu abubuwa da a ka nuna a fim ɗin a zahirance ba za su faru ba.
Allahu a’alamu.
No comments:
Post a Comment