Tuesday, November 14, 2017

Hanyoyi 5 da gwamnati za bi don samun kudaden da za ta yi ayyukan dake kasafin kudin 2018



Ministan kasafin kudi da tattalin arzikin kasa Udo Udoma ya zayyano hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen samar da kudaden da za ta yi ayyukan da ta sa a kasafin kudin 2018.
Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na naira Tiriliyan 8.6 ga majalisar kasa a makon da ya gabata.
Ga hanyoyin
1 – Na farko za mu kara tsannanta wa wajen karbar haraji sannan zamu kara kudaden shiga ta hanyar karban haraji zuwa kashi 15 bisa 100 daga kasha 6 bisa 100.
2 – Za mu yi amfani da kudaden da muka samu a mai wajen bunkasa fannin da ban a mai ba, daga nan sai muyi amfani da ribar da zamu samu ta hanyoyi biyu Kenan wajen samar da ababen more rayuwa.
3 – Zamu kirkiro wasu hanyoyi da za a dunga samun kudaden shiga a kasar na da za ay amfani da ilimin kimiyya wajen tara kudaden, haraji da bin diddigi sanna kuma zai taima ka wajen gano masu kin biyan haraji.
4 – Gwamnati za ta sake duba yadda kamfanoni ke gudanar da ayyukan su a yankunan da ake hako danyen mai. Za a sake duba shiri da bayanai game da yadda ake sabunta lasisin kamfanonin da tsawon kwanankin da za a yi kafin a sake duba haka. Bayan haka kuma za a sake komawa teburin shawara da sabunta yanjejeniya da ke tsakanin kamfanonin main a kasahesn waje da Najeriya domin inganta samun kudaden shiga.
5 – Duk da cewa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati suna kokari wajen samar da kudaden shiga ta hanyar karban haraji, sai sun kara matsawa sosai idan har anaso a cimma burin da aka sa a gaba.
Za a kara seta su domin ganin ba a samu Baraka ba da kuma like duk wata rami da zai iya sa a samu matsala a haka.

No comments:

Post a Comment

Pages