Tuesday, November 21, 2017

2019: Kwankwaso Ne Mafi Dacewar Shugabancin Nijeriya, Inji Bakin-Zuwo



A yayin da babban zaben 2019 ke kara gabatowa kusa; an bayyana Tsohon Gwamnan Jihar Kano a matsayin mafi cancanta kuma mafi dacewar zama Magajin Shugaba Muhammadu Buhari.
"Shakka babu idan a na maganar cancanta, idan a na maganar sanin salon mulki nagari, lakantar hanyoyin bunkasa kasa, kawar da matsalolin al'umma da inganta jin dadinsu ta hanyar share masu hawaye to babu kamar ko irin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin matashin dan kasuwar Kasa da Kasa Alhaji Yusuf Yunusa Bakin -Zuwo a tattaunawarsa da RARIYA a karshen makon nan.
Ya ce Sanata Kwankwaso wanda ke da kwarewa da gogewa a fannin siyasa da mulki haka ma cikakken dan akidar siyasa ne wanda karan zubin siyasarsa ya yi canjars da siyasar akida ta son ci-gaba da bunkasar al'umma.
"Jagoran Kwankwasiyya ya san ciki da wajen siyasa, kashe-kashenta, tasirinta da matsalolinta, ya san Nijeriya da al'ummarta kamar kuma yadda ya riga ya san matsalolin kasa da 'yan kasa tare da tanadar hanyoyin magance su." Ya bayyana.
Bakin- Zuwo wanda shine Mataimakin Ko'odinetan fitacciyar kungiyar nan da ta yi fice wajen tallata manufofin siyasar Kwankwasiyya wato 'Save Nigeria Project' reshen Jihar Kano ya bayyana cewar Kwankwaso ya shirya tsaf domin kai Nijeriya da al'ummarta a tudun mun tsira.
"Nijeriya a yau ta na bukatar hazikin shugaba, jajirtacce mai kishi da sanin ya kamata wanda a jiya da yau a ka auna mulkinsa da siyasarsa a saman sikeli aka kuma tabbatar ya taka muhimmiyar rawa a kai."
A cewarsa Sanata Kwankwaso ya ciri tuta ya kuma samarwa kansa suna a matsayin shugaba daya tilo irinsa na farko da ya canza fasali da alkiblar Jihar Kano ta hanyar gudanar da mabambantan ayyukan da suka daukaka Kanon- Dabo har ta kara yi wa takwarorinta nisa.
Bakin- Zuwo ya bayyana cewar Akidar Kwankwasiyya ta samu gagarumar karbuwa daga Arewaci zuwa Kudancin kasa saboda yadda jama'a ke kallon Kwankwaso a matsayin dan kishin kasa wanda ke fafutukar ganin talakawan Nijeriya da al'ummarta bakidaya sun samu kyakkyawar makoma.
Ya ce karbuwar da Kwankwasiyya ta samu a fadin kasa bakidaya al'amari ne na Allah wanda za a kara yi wa mai kowa mai komai godiya ta hakika kuma alamomi ne da ke tabbatar da cewar Juma'ar da za ta yi kyau ce al'umma suka fara gani tun daga ranar Laraba. Ya kara da cewar idan har al'umma suka kara bayar da cikakken goyon baya aka kawar da kowane irin bambanci aka hada kai aka yi aiki tare domin ceto Nijeriya to za a cimma biyan bukatar da ake bukata ta tabbatar da zaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin zababben Shugaban Kasa a ranar 29 ga watan Mayu 2019.w

No comments:

Post a Comment

Pages