Bashir wand makiyayi ne shi, yace Yan Boko Haram sun shigar dashi kungiyar ne yayin wata fita da yayi zuwa daji watanni 8 da suka wuce, kuma yace tun daga wannan lokaci mutane 2 kawai ya kashe.
Asali na dan jihar Nassarawa ne, kuma mahaifina ne ya kore ni sakamakon yadda nake yawan kadaicewa ni ka dai. Waus daga cikin mu sun kutsa kai zuwa yankin kudu maso yammacin kasar nan, kuma akwai wasu manyan masu kudi ne ke bamu makamai.” Inji shi. Bashir shine mutum na 165 cikin jerin yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, kuma an kama sh ne a daidai wajen da aka kama dan Boko Haram na 156 da Sojoji ke nema ruwa a jallo. Shima kwamishinan Yansandan jihar Ondo ya tabbatar da cewa Bashir dan Boko Haram ne, kuma yana daya daga cikin almajiran wani kwamandan Boko Haram mai suna Daffo, daya daga cikin makusantan Shekau. Naijhausa
No comments:
Post a Comment