Masarautar kano ta musanta labarin dake yaduwa a kafafen yada labarai daban daban na kasa, wanda ke cewa masarautar ta ba mawakin kudu, Korede Bello, sarautar sarkin wakar Kano. Dan Buram Kano, Alhaji Munir Sanusi wanda shine shugaban ma’aikatan masarautar Kano ya musanta labarin ne game da labarin da ke bazuwa a kafafen yada labarai daban daban na kasa dake cewa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ba mawakin, Korede Bello, sarautar sarkin wakar Kano Ya ce saboda haka masarautar Kano ba ta da niyyar yin haka sannan kuma ba ta yi magana da mawakin akan faruwan haka ba, saboda haka duk labarin dake yaduwa duk cece-ku ce ne sannan kuma ba ta da wani asali. An samu labarin cewa daya daga cikin ‘ya’yan Sarkin Kano ya gaiyace mawakin Kudun hawan sallar Eid-Kabir, inda mawakin yayi hawa tare da shigar ‘yan sarauta. Bincike ya nuna cewa a lokacin da aka ga mawaki a bisa kan doki tare da shigar masarauta shine mutane ‘yan kallo suka kama kiran shi sarkin wakar Kano
No comments:
Post a Comment