Jigo Kuma Uba A Jam'iyyar PDP, Sanata Danladi Sankara, Tsohon Sanatan Jigawa Ta Yamma,Ya Koma Jam'iyyar APC Tare Da Magoya Bayansa Fiye Da Mutane Dubu Dari Biyar. Maigirma Sen Danladi Sankara Dama Shine Kadai Ya Rage A Cikin Mutane Da Suke Da Dubban Al'ummar A Cikin Jam'iyyar PDP A Jihar Jigawa. Kafin Ficewar Tashi Sai Da Jam'iyyar PDP A Jihar Jigawa, Ta Tura mishi Mutane Domin Ba shi Hakuri Akan Kada Ya Fice Daga Jam'iyyar, Haka Zalika Ita.ma Jam'iyyar APC Ta Tura mishi Wasu Jiga-Jigan Jam'iyyar Domin Su yi Zawarcinsa Zuwa Jam'iyyar Ta su Ta APC. Ficewar Tashi Za ta Sake Jefa Jam'iyyar PDP Cikin Rudani A Jihar Jigawa. Ko A Shekarar Da Ta Wuce Sai Da Jiga-Jigan Jam'iyyar Ta PDP Irin su Ambasada Ahmed Abdulhamid Mallammadori Tsohon Minista, Alhaji Jumbo Kazaure, Alhaji Yahaya Bigman, Alh Khalid Birnin Kudu, Hon Muhammad Ahmed Gumel Tsohon Maitaimakin Gwamna A Lokacin Mulkin Sule Lamido, Suka Fice Su da Magoya Bayansu Zuwa Jam'iyyar APC.
No comments:
Post a Comment