Sunday, October 1, 2017

Dalilin da yasa sabuwar yar fim ta zama jarumar shirin “Mansoor”


Sabuwar tauraruwar fim din Hausa na masana’antar Kannywood Maryam Yahaya wanda ta samu suna bayan fittowar ta a cikin shirin “Mansoor” ta bayyana cewa shirin shine fim na farko da ta fara yi kuma ba a dalilin ta aka shirya fim din. Ta bayyan a haka a wata hira ta musamman da tayi da BBC hausa . Ta shaida wa BBC hausa cewa sai da Ali Nuhu ya yi magana da iyayen ta kana ta fara fitowa a fim. “Tun ina yar karama nake sha’awar yin fim har na girma nace zan fara yin fim amma babana yace gaskiya bazan yi fim ba, inata cewa inaso shikuma ya nace cewa ba zan yi ba, kawai sai na hakura, domin ko naje nayi bazan ji dadi ba saboda basu son inyi”. “Yanda aka barni na fara yin fim shine, sarki Ali Nuhu yace min zai je gidan mu yayi magana da babana. Bayan ya ganshi shine babana yace mai gani nan ya barni nayi fim kuma ya bashi ni amana, shine yace toh ba komai” , tace. Jarumar tace ba dalilin ta aka rubuta fim din "Mansoor" amma dai asali tana cikin yan wasa da zasu fito a shirin. Ta kasance jarumar shirin sanadiyar rashin zuwan ainihin jarumar da za’a amfani da ita wurin hada shirin. Tana cewa; “Bayan mun je wurin muka ji shuru-shuru, wanda za’a saka a shirin bata zo ba, ana ta jiran ta bata zo ba. Wurin kuma dama akwai mata da yawa, sai Ali Nuhu yasa gabadaya aka kira mu sai ya zabe ni da wata ya bamu script mu karanta kuma bayan minti biyar muzo mu gwada mashi. Bayan nayi scene da yace muyi kawai sai na gan mutanen wurin suna ta dariya, suna ihu kawai sai naji ance mun to inje in fara aiki”. Jarumar “Mansoor” tace shirin ya bude mata hanya wajen fitowa a wasu fina-finai da dama.

No comments:

Post a Comment

Pages