Tuesday, October 3, 2017

Dalilin da ka iya sa PDP yanke shawarar tsayar da Makarfi takarar shugabancin kasa a 2019


Akwai alamun cewa jam’iyyar PDP ka iya tsayar da Ahmed Makarfi a matsayin dan takarar ta zaben shugabancin kasa na 2019 - An ce tuni wasu manyan jam’iyyar sun fara yi ma Makarfi yakin neman zabe a sirri - wadannan manya sun hada da gwamnoni da tsoffin gwamnoni na cikin jam’iyyar Babu mamaki Jam’iyyar PDP ta yanke hukuncin tsayar shugaban jam’iyyar mai ci, Ahmed Makarfi a matsayin dan takarar ta na shugabancin kasa a zaben 2019. An rahoto cewa wata kungiya mai karfi a cikin jam’iyyar sun fara gudnar da yakin neman zaben shugabancin kasa a madadin Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna.
Kungiyar wace ta tattara gwamnoni masu ci a yanzu da kuma tsofaffin gwamnoni, suna so Makarfi ya zamo dan takarar shugabancin kasa na PDP. An kuma tattaro cewa yayinda PDP ta mika tikitin dan takarar shugabancin 2019 ga arewa, shugabancin jam’iyyar zai koma kudu maso yamma.

Wata majiya tace yan jam’iyyar da dama sun amince da cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna baida wani nauyin siyasa sannan kuma cewa hakan zai basu damar yakin neman zabe cikin sauki da suka nasarar jam’iyyar a 2019. Koda dai Makarfi bai nuna ra’ayin tsayawa takara a zabe mai zuwa ba, maganganu sun nuna cewa zai yi nasara a kan shugaba Muhammadu Buhari. A baya Hausazone.com ta kawo cewa gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kaddamar da ra’ayinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019.

No comments:

Post a Comment

Pages