Idan har yankin catalunya ya balle daga kasar Spaniya Barcelona tana bukatar ta samu inda zata dunga buga gasar rukini-rukuni, hakan yana nufin dole sai dai a kafa sabuwar gasa a yankin na catalunya sannan kuma a samu kungiyoyin da zasu dunga fafata gasar. Dole sai sun kai adadin wasu kungiyoyi sannan hukumar kwallon kafa ta duniyazata yarda tayi musu rijista haka itama hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai. A halin yanzu kungiyoyi uku ne kawai suke wakiltar yankin na catalunya a gasar laliga, Espanyol da Girona sai kuma Barcelona, hakan yana nufin dole sai sun sake sababbin kungiyoyi idan har suna son su fara gasa tasu ta kansu. Idan kuma ba hakaba dole sai dai Barcelona ta koma kasar faransa domin cigaba da buga gasar kasar, domin dole sai sunada manyan kungiyoyi wadanda zasu iya jurewa sannan sai sunada karfin tattalin arzikin da zasu iya rike kansu. Har ila yau, ballewar Barcelona zai rage musu karfi wajen fafatawa a duniya, domin zasu mamaye sabuwar gasar dazasu kafa hakan zaisa su raina kowa a kasar sannan zasu dena siyan manyan wasa domin zasu raina gasar, inda a karshe kuma manyan yan kwallo zasu dena shiga kungiyar saboda babu kalubale sannan kuma yanayin haska gasar tasu zai ragu tunda babu manyan yan kwallo.

No comments:
Post a Comment