Tare Da: Saddika Habib Abba
Suna: Kalan dangi
Tsara labari: Fauziyya D Sulaiman
Furodusa: Abubakar Bashir Mai Shadda
Director: Ali Gumzak
Kamfani: Tsamiya Inbestment
Jarumai: Ali nuhu, Aminu Sharif Momo, Sadik S Sadik, Sani Idris Moda, Baballe Hayatu, Aisha Aliyu Tsamiya, Jamila Nagudu, Hafsat Idris, Maryam Booth, Hajara Usman, Hadiza Muh’d, Rabi’u Rikadawa, Ibrahim Mandawari. A farkon fim din an nuna gidan wani attajirin mai kudi Alh.Mu’azzam Canji (Ibrahim Mandawari) shine shugaban ‘yan caji yana zaune a gidansa tare da matarsa (Hajara Usman) da kuma ‘ya’yansa Guda biyu mata Fadila (Jamila Nagudu) da kuma kanwarta Kubra (Maryam Booth) an nuna cewar ita Fadila ‘yar karyace ‘yar nuna son a sani ce sannan kuma ta tsani talaka tana kyamatarsa in har ya rabeta, ita burinta ta auri me kudi, sai ita kanwarta ta Kubra ita babu ruwanta da nuna ita mai kudi ce sannan tana da saukin kai kuma tana harka da talaka,
Sai kuma bangaren masu aikin gidan (Rabi’u Rikadawa) shine mai gadin gidan da matarsa Marka (Hadizan Saima) da ‘ya’yansu ‘yan mata guda uku duk a gidan suke zaune akwai Samira (Aisha Tsamiya) da kuma Salma (Fati Washa) da kuma (Hafsat Barauniya) amma dukkansu ‘ya’yan makaryata ne burinsu suyi wa samari karya sannan su auri mai Kudi guda daya ce rak ta kirki ( Hafsat Barauniya) itace bata goyon bayan abinda suke yi sakamakon hakan ya haifarmata da tsana a wurin mahaifiyarta Marka saboda ita ma mahaifiyar mai idon cin naira ce burinta ‘ya’yanta su auri mai kudi a gurin mahaifinsu Mai gadi kadai ta ke samun sassauci domin shi sam baya bin bayan abinda suke yi matar tasa ta fi karfinsa ne kawai, Salma da Samira har kwalliya suke su tafi jami’a da wurare na shakatawa su hada baki da direban gidan Mado (Musa Mai Sana’a) ya daukesu yana zazzagawa dasu acikin mota domin masu kudi su gansu suce suna san su idan sun dawo zu kawo kudi su bawa Mado don dama kafin su fita sai sun yi ciniki.
Sai bangaren Adamu (Ali Nuhu) wanda yake aikin direba a gidan Alh.Sabo (Baballe Hayatu) shima babu abinda yake yi sai karyar arziki idan ya dauki mota sai yaje yana yiwa ‘yan mata karyar cewa motarsa ce domin yayansa shine shugaban ‘yan kasuwa a haka har suka hadu da Samira suka fara soyayya domin kowannensu yana zaton me kudi ne. sai kuma bangaren Habu (Aminu Sharif)wanda yake zaune cikin talauci da kakarsa kullum mafarkinsa ya zamto mai kudi ya dinga hawa manyan motoci sannan burinsa iri daya tare da wani Abokinsa Tukur (Sadik Sani Sadik) wanda yake shi almajiri ne ma amma babu abinda suka saka a gaba sai son su zama masu kudi domin su dinga yiwa ‘yan mata karya ana cikin haka sai wataran Habu yazo gida ya tarar ankawo wa kakarsa kayan abinci na zakka ya tambayeta waya kawo tace masa Alh.
Sunusi ne nan fa Habu ya fara tsalle da murnar ashe dama a danginsu akwai mai kudi bata taba fadamasa ba tace masa ba d’an uwanta bane sun yi zaman makota ka ne tare da kakarsa shi kuma a lokacin yana yaro Habu ya fara tsalle da murnar ai dan uwansu ne duk da haka ba da bata lokaci ba ya nemi kwatancen gidan Alh. Sunusi ya je ya yi masa bayani da farko bai gane shi ba sai da ya yi masa bayanin ai shi jikan mai kosai ne wadda ya kawo wa zakka dakyar Alh. Sunusi ya gane sannan ya daukeshi aiki har yake bashi motarsa yana hawa anan Habu ya sake samun lasisin yiwa abokai da ‘yanmata karya abotarsu da Tukur ta sa ke kulluwa a haka har Habu ya hadu da Salma suka fara soyyaya ita a zaton ta mai kudi ne shi kuma a zatonsa ‘yar Alh.
Mu’azzam canji ce domin haka tace masa haka suka cigaba da yiwa juna karya.
A bangaren gidan Alh. Sabo kuwa matarsa bata haihuwa har ya yi yunkurin kara aure ya hadu da Fadila ta nuna cewar ita bata harka da talaka domin duk ita a zaton ta talaka ne bata san babban me arziki bane shi yasa taci zarafinsa har ya hakura da neman aurenta wannan abinda ta yi masa shine ya yi masa ciwo ya sanya suka hada baki da abokinsa Alh.
Sunusi domin a nemo yaro dan karya a biya shi yaje ya yaudari Fadila da cewar shi mai kudi ne idan yaso bayan auren sai ya bayyana mata kansa domin ta gane kuskurenta, Alh. Sunusi ya sanya Habu ya nemo musu yaro Habu kuwa ya nemo abokinsa Tukur su Alh. Sabo suka yaba da Tukur sannan suka ba shi manyan motoci da kaya masu kyau domin ya je ya sato zuciyar Fadila haka kuwa aka yi domin Fadila tana ganinsa da wannan manyan motocin ta rude ta amshi soyayyarsa suka kulla, ana cikin haka sai Alh. Sabo ya kuma haduwa da kanwar Fadila Kubra itama ya nuna yana sonta cikin girmamawa ta amshi soyyarsa. Alh. Mu’azzam Canji kuwa ana haka sai ya umarci duk ‘yan matan gidansa su fito da mijin aure kowacce ta fadawa na ta saurayin kowannensu kuwa ya fito shi Adamu ya yi hayar waliyyai da kayan aure Tukur da Habu kuwa Alh. Sabo ya yi musu komai aka zo aka daura aure sai bayan an daura a gurin fatin bikin kuma duk asiri ya tonu shi Tukur da kansa ma ya ta shi ya bayyana ko shi wanene su kuma ragowar wasu mata ne da Mado direba suka zo suka tona asiri a gurin fatin hankalin kowannesu ya tashi har da masu cewar sun fa sa.
Abubuwan Birgewa:
1- An yi amfani da kayan aiki masu kyau a labarin.
2- shirin ya tabo wata matsala da take faruwa a wannan zamanin kuma an nuna wa masu irin wannan dabi’ar illar ta.
3- Jaruman kowannensu ya yi matukar kokari wurin isar da sakon. Kurakurai:
1- Akwai wurin da aka ga abun daukar sauti ya fito a jikin Habu.
2- ‘ya mace ‘yar kwalliya ce amma kwalliyar da aka din ga nu no wa a fuskokin duk jaruman mata a kodayaushe da kowanne irin lokaci ta yi yawa don bazai yu ace kullum mutum da kwalliya ba irin wannan babu wani ranar hutu an nuna kamar ana nuna wa masu kallo su ga kwalliyar ne.
3-Bazai taba yi wu wa a gaske ace suna yin wannan karyace karyacen kuma duk sun nemi aure a gida daya ba amma asirinsu bai taba to nuwa ba, shin a auren babu bincike da akayi? kawai auren aka yi?
4- Shin dama Mado direba mawaki ne ? ko kuma M.C ne? a fim din direba kawai aka nuna yana yi amma sai ga shi an ganshi a wurin biki yana M.C kuma yana waka.
5- Sutturar matan masu kudi manyan lesina ne da atamfofi manya amma yanda ake kuranta kudin Alh. Mu’azzam gidan da aka nuna yana ciki da sutturar da ‘ya’yansa da matarsa suke sakawa ya yi Kadan a yanda ake bayyanar da arzkinsa.
6- Akwai wurin da Alh. Sabo ya ke fadawa Alh.Sunusi ya hadu da Fadila a jami’a ta wulakanta shi a gaban mutane ta saka ana kallonsa amma masu kallo sun san wurin da aka nuna sun hadu ba jami’a bane kuma wurin babu kowa sai su kadai amma har ya ce jama’a suna kallonsa.
7-Ka’ida idan za’ayi aure kowa yasan kafin akai ga daurin aure ake zuwa ganin wurinda amarya za ta dauna amma sai ga shi an nuna sai bayan daurin aure aka nuna an zo gidan Habu ganin dakin Salma
8- Akwai wurin da Marka ta ke fadawa mijinta kayan abincinsu ya kare har Hajiya take fadin ta dibi na su kowa ya san masu aikin da suke zaune a gidan iyayen gidansu ba sa siyan abinci a gidan ake fitar musu ballantana su Marka da suke gidan tsahon shekara Ashirin da wani abu.
9- Habu da Tukur kowa ya san basu yi karatun boko ba saboda babu hasali ma shi Tukur kolo ne amma sai ga shi idan sun je wurin ‘yan matansu suna yi musu turanci mai kyau bana dan koyo ba.
10- A irin arzikin Alh.Mu’azzam bai kamata ace direba daya ba ne kuma motar da ake fita da ita daya ba ce da har idan aka sami matsala ‘yarsa za ta fita ta hau adaidaita sahu kamar yanda Kubra ta yi lokacin da Mado ya ce Mota ta sami matsala. Karkarewa:
Labarin ya kayatar kuma ya bai wa mutane dariya, amma kuma karyace-karyacen da a ka nuna babu yadda za a yi a gaske su faru kuma har a yi auren asiri bai tonu ba. Wallahu a’alamu!
No comments:
Post a Comment