Monday, October 2, 2017

Abin da muka yi a fannin tsaro tunda muka hau gwamnati – Buhari


Shugaban kasa uhaadu Buhari yayi tsokaci akan gudunawar da gwanatinsa ta taka a fannin tsaro tun bayan karbar mulki daga hannun ja’iyyar PDP a shekara ta 2015. A cewar shugaban kasar: “A sashin tsaro, ya zama wajibi ga ‘yan Najeriya da su yi shukura da jinjina ga zaratan sojojin Najeriya da suka jajircewa wajen shigewa gaba domin ganin sun fatattaki mayakan Boko Haram. A yanzu sun kai Boko Haram makurar kakkabe su, sun boye sai dai su rika kai harin sari-ka-noke kawai a daidaikun wurare. "Najeriya na godiya ga kasashe makwabta da kuma kungiyoyin kasa da kasa wadanda su ka taimaka wajen ganin mun cimma kudirin mu na kakkabe burbushin Boko Haram. Wannan matsalar ta’addanci ta addabi hatta manyan kasashen Turai da wasu yankuna masu ingantaccen tsarin ‘yan sanda, su ma sai da ta’addanci ya zame musu karfen-kafa. KU
"Ba mu bar sojojin mu baya ba wajen inganta ayyukan su, ta habbaka OPERATION LAFIYA DOLE, mun kuma kafa dakarun kai farmakin gaggawa a Arewa maso Gabas. Wannan ne zai kawo yunkurin da mu ke yi na karshen ganin bayan Boko Haram." A wani al’amar na daban mun ji labarin cewa Kungiyar IPOB ta Biyafara za ta maka tsohon Gwamnan Jihar Abia da Janar Tukur Buratai a Kotu.
Kungiyar IPOB za ta maka tsohon Gwamnan Abia da Janar Buratai a Kotu 'Yan Biyafara za su shigar da Buratai kara a Kotu 'Yan Biyafara su na kukan bacewar Jagoran na su Nnamdi Kanu wanda har yau ba a san inda yake ba kamar yadda Sakataren Kungiyar Emma Powerful ya bayyana. Ya kara da cewa za su shiga Kotu da Shugaban Hafsun Sojin kasar Janar Tukur Buratai domin ya fito ta Nnamdi Kanu. Tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu wanda su ke zargi da kokarin yi wa 'Yan Kungiyar su kisan gilla domin ya burge mutanen Arewa da kuma cewa ba zai rasa sanin inda aka boye Nnamdi Kanu ba.

No comments:

Post a Comment

Pages