Wannan matsalar ta’addanci ta addabi hatta manyan kasashen Turai da wasu yankuna masu ingantaccen tsarin ‘yan sanda, su ma sai da ta’addanci ya zame musu karfen-kafa. KU "Ba mu bar sojojin mu baya ba wajen inganta ayyukan su, ta habbaka OPERATION LAFIYA DOLE, mun kuma kafa dakarun kai farmakin gaggawa a Arewa maso Gabas. Wannan ne zai kawo yunkurin da mu ke yi na karshen ganin bayan Boko Haram." A wani al’amar na daban mun ji labarin cewa Kungiyar IPOB ta Biyafara za ta maka tsohon Gwamnan Jihar Abia da Janar Tukur Buratai a Kotu.
Kungiyar IPOB za ta maka tsohon Gwamnan Abia da Janar Buratai a Kotu 'Yan Biyafara za su shigar da Buratai kara a Kotu 'Yan Biyafara su na kukan bacewar Jagoran na su Nnamdi Kanu wanda har yau ba a san inda yake ba kamar yadda Sakataren Kungiyar Emma Powerful ya bayyana. Ya kara da cewa za su shiga Kotu da Shugaban Hafsun Sojin kasar Janar Tukur Buratai domin ya fito ta Nnamdi Kanu. Tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu wanda su ke zargi da kokarin yi wa 'Yan Kungiyar su kisan gilla domin ya burge mutanen Arewa da kuma cewa ba zai rasa sanin inda aka boye Nnamdi Kanu ba.
No comments:
Post a Comment