Gwamnatin Najeriya a watan Yuli ta sakar wa jihohi N243.79 biliyan a karo na biyu daga cikin kun da aka dawo da shi na Paris Club. A karon farko ta saki N388.30 biliyan a watan Disamba na bara. Gwamnatin tarayya ta saki wannan kudin ne a sakamakon ca da gwamnatin jihohi suka yi mata a kan ana ta ragar kudin da ake basu tun 1995 zuwa 2002 don a biya bashin kasa. Gwamnatin tarayya ta umarci gwamnatin jihohi da su biya basussukan albashi da fansho da ma'aikatan su suke bi. NAN ta ce a binciken da ta yi, jihohi 15 daga cikin 22 ne suka biya ma'aikatan su. Ragowar kuma sun karba sun yi shiru.
No comments:
Post a Comment