Wasu sun biya basussukan albashin ma'aikata da fansho - Wasu jihohin kuma sun soke sun yi shiru - Me ya kamata ayi da su? Mafi yawancin jihohin Najeriya sun yi amfani da kudaden Paris Club don su biya ma'aikatan da ke bin bashin albashi da kuma 'yan fansho. Amma duk da haka a jihohi da dama har yanzu akwai ma'ikatan da suke bin bashin albashin nasu. A wani bincike da wata kungiyar manema labarai (NAN) ta yi, ta ce masu bin bashin ya kama daga albashin wata biyu har zuwa wata goma sha daya.
Gwamnatin Najeriya a watan Yuli ta sakar wa jihohi N243.79 biliyan a karo na biyu daga cikin kun da aka dawo da shi na Paris Club. A karon farko ta saki N388.30 biliyan a watan Disamba na bara. Gwamnatin tarayya ta saki wannan kudin ne a sakamakon ca da gwamnatin jihohi suka yi mata a kan ana ta ragar kudin da ake basu tun 1995 zuwa 2002 don a biya bashin kasa.
Gwamnatin tarayya ta umarci gwamnatin jihohi da su biya basussukan albashi da fansho da ma'aikatan su suke bi. NAN ta ce a binciken da ta yi, jihohi 15 daga cikin 22 ne suka biya ma'aikatan su. Ragowar kuma sun karba sun yi shiru.
No comments:
Post a Comment