Tsohon shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa, Kasimu Yero ya rasu, kamar yadda wani na kusa da marigayin ya shaida wa BBC. Marigayin ya rasu ne ranar Lahadi a garin Kaduna a arewacin Najeriya bayan ya yi doguwar jinya. Ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai ta kasar wato NTA - a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci) da Karanbana da dai sauransu.

Ana ci gaba da mika sakon ta'aziyya game da rasuwar dan wasan wanda ya shahara wajen barkwanci. Jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya yi fatan Allah Ya jikan marigayin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
No comments:
Post a Comment