Ministan Labarai da al'adu ya karyata rahoton zuwan Buhari Amurka gobe - Kwana nan Amurka ta sayarwa da Najeriya manyan jiragen yaki Ministan Labarai da al'adu ya karyata rahoton zuwan Buhari Amurka gobe. Ministan yace wannan labari ba gaskiya bane a wani jawabi da aka saki a jihar Legas. Da safiyan yau mun bada labarin cewa shugaba Buhari na shirin tafiya Amurka gobe, 4 ga watan Satumba, 2017. Wannan ziyara da shugaban kasan Najeriya zai kai bisa ga wata goron gayyata da shugaban kasan Amurka Donald Trump ya aiko masa da shi ne tun wata Fabrairun wannan shekarar. Amma kamar yadda muka sani lokacin ya fara rashin lafiya.

Game da cewar jaridar Sahara Reporters, shugaba Buhari bar gida Daura misalign karfe 9:15 na safe a jirgi mai saukar angulu zuwa filin jirgin saman jihar Katsina inda zai tashi misalign karfe 10 na safe zuwa Amurka.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa abinda aka shirya a da shine shugaba Buhari ya hada tafiyar da taron gangamin majalisar dinkin duniya da za’ayi ranan 21 zuwa 25 na watan Satumban 2017. Amma wata majiya na cewa da alamun akwai kishin-kishin jinya a cikin tafiyar.
-Naijhausa
No comments:
Post a Comment