Monday, September 4, 2017

Kamfanin Shirya Finafinai Mallakin Rahama Sadau Zai Koma Shirya Finafinansa


Kamfanin Shirya Finafinai Mallakin Rahama Sadau Zai Koma Shirya Finafinansa Daga Mujallar Fim Fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa Rahma Sadau, za ta ci gaba da shirya finafinai nata na kanta a kamfanin ta na "SADAU PICTURES" Kuma jarumar ta bi hanyoyi iri daban-daban domin tallata fina-finanta a wajen masu kallo. Wannan matakin ya biyo bayan dagewar da hukumar tantance finafinai ta yi ne a kan kin tantance duk wani fim da aka sa jarumar a ciki, wanda hakan ya tilastawa masu shirya finafinai daina sa jarumar a fina-finan su, don gudun samun matsala. Yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin fara daukar wani sabon fim na kamfaninta bayan RARIYA wanda aka haska a wasu manyan gidajen sinima na kasar nan. Ba wani sabon labari ba ne cewa Rahama Sadau yanzu ta fi fitowa a finafinan kudu na Turanci wanda ya zuwa yanzu ta yi fim da yawa daga ciki akwai, Son of the Caliphate season 1&2, The light will come, Ajuwaya, Hakkunde da kuma shirin talabijin na Super Story tare da Sani Danja. Akwai kuma wani sabon shirinta da zai fito ranar 8 ga Satumbar da muke ciki mai suna TATU wannan fim abin kallo ne domin abubuwan mamakin da suke ciki, fim din ya tara manyan jaruman kudu. A kwanakin baya ne kuma jarumar ta je Amurka, don yin wani fim tare da fitaccen mawakin nan Akon, mai suna American King. Korar jarumar dai daga industirin Hausa fim ya zama mata kamar wani gobarar titi ne a Jos, domin ko a kwanaki baya ma babbar jaruma Priyanka Chopra ta kasar Indiya ta bayyana aniyarta na son haduwa da Rahama Sadau. A yanzu haka jarumar ta gama daukar wani sabon shirin kamfanin 2effect na turanci mai suna Fantsatic 4 tare da Yakubu Mouhammad. ©Zuma Times Hausa

No comments:

Post a Comment

Pages