Tuesday, September 5, 2017

Gwamnatin Buhari ta sai wa Nnamdi Kanu gida a Landan — Uwazuruike


Nnamdi Kanu gwamnatin Buhari yake yiwa aiki don kashe maganar neman 'yancin Biafra - Sun rufe masa ido da kudi da gidaje a kasashen waje - Su suke sa shi yake yin abubuwan da yake yi don a ce masu neman 'yanci Biafra ba su bi hanyar dai-dai ba Wanda ya samar da kungiyar neman 'yancin kasar Biafra (MASSOB), Ralph Uwazuruike, ya ce gwamnatin Najeriya ta riga ta siye mai jagorantar kwatar kasar Ibo, Nnmadi Kanu. Ya ce har sun sai masa gida a Birnin Landan. Ya ce, "Gwamnatin Buhari ta tunkari Kanu da tukwicin da ba kowa bane zai iya kin karba ba don ya yiwa neman 'yancin Biafra zabon kasa. Gaskiyar lamarin zai fito kome daren dadewa. "Sanda Kanu ya ce kar a fita ayi zabe a Jihar Anambra a watan Nuwamba na bara makarkasa ce don jam'iyyar APC ta samu kujerar gwamna a jihar. "Kanu bai san bambancin zaben kujerar siyasa ba da zaben neman 'yanci. Kuma ya ingizo 'yan Ibo da kalaman tarzoma don su nuna zasu kwaci Baifra ta karfi da yaji. Zai janyo 'yan Ibon da ke zama a Arewa su rasa rayukan su a banza da wofi." DUBA WANNAN: Sharo: Saurayi ya rasa ran sa wajen neman aure Uwazuruike ya ce 'yan Ibo bai kamata suna koyi da Kanu ba. In ana neman 'yancin kasa ba da fada ake kwata ba. Maganganu za ayi ta yi na hankali har sai an karba.

Uwazuruike ya ce 'yan Ibo bai kamata suna koyi da Kanu ba. In ana neman 'yancin kasa ba da fada ake kwata ba. Maganganu za ayi ta yi na hankali har sai an karba.

Source -Naijhausa

No comments:

Post a Comment

Pages