Ya ce, "Gwamnatin Buhari ta tunkari Kanu da tukwicin da ba kowa bane zai iya kin karba ba don ya yiwa neman 'yancin Biafra zabon kasa. Gaskiyar lamarin zai fito kome daren dadewa. "Sanda Kanu ya ce kar a fita ayi zabe a Jihar Anambra a watan Nuwamba na bara makarkasa ce don jam'iyyar APC ta samu kujerar gwamna a jihar. "Kanu bai san bambancin zaben kujerar siyasa ba da zaben neman 'yanci. Kuma ya ingizo 'yan Ibo da kalaman tarzoma don su nuna zasu kwaci Baifra ta karfi da yaji. Zai janyo 'yan Ibon da ke zama a Arewa su rasa rayukan su a banza da wofi." DUBA WANNAN: Sharo: Saurayi ya rasa ran sa wajen neman aure Uwazuruike ya ce 'yan Ibo bai kamata suna koyi da Kanu ba. In ana neman 'yancin kasa ba da fada ake kwata ba. Maganganu za ayi ta yi na hankali har sai an karba. Uwazuruike ya ce 'yan Ibo bai kamata suna koyi da Kanu ba. In ana neman 'yancin kasa ba da fada ake kwata ba. Maganganu za ayi ta yi na hankali har sai an karba.
Source -Naijhausa
No comments:
Post a Comment