Wednesday, September 6, 2017

Dandalin Kannywood: babban dalilin da ya hana a ida yin fim din nan na Boko Haram


A kwanan baya ne dai muhawa ta dauki zafi a kafafen sadarwar zamani biyo bayan wata fasta da ta fara yawo dauke da hoton Jarumin nan na masana'antar fina-finan Hausa Sadiq Sani Sadiq sanye da tufafi sak irin na shugaban kungiyar nan ta ta'addanci na Boko Haram. To sai dai kuma tsawon lokaci bayan faruwar hakan har yanzu ba'a kara jin duriyar masu shirya fina-finan ba ko kuma shi jarumin game da dalilin hakan. Read more: Kannywood zasu shirya fim mai kwai kwayon boko Haram

Majiyarmu da ta ji shiru shine ta shiga bincike inda ta samu daga majiyar mu ta mujallar fim da tayi fira da babban furodusan fim din Umar Uk ya bayyana cewa cece-kuce ne yayi masu yawa inda mutane suka rika kiran su suna rokon su da su dakatar da shirin. Furodusan ya bayyana cewa sun samu kira ba adadi daga jama'a da dama ciki hadda manyan jaruman fim kamar su Ali Nuhu da Adam A. Zango inda suka roke su da su taimaka su dakatar da yin fim din.

No comments:

Post a Comment

Pages