NAIJ.com ta samu dai cewa jarumar tace kwarai akwai masu aikata masha'ar a cikin su amma ba yana nufin dukkan su haka suke ba. Ta ce: "kamar yadda akwai su a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata a yi mana kudin-goro ba." Jarumar ta kuma roki jama'ar gari masu kallon su da su rika yi masu uzuri akan al'amuransu kasantuwar su ma mutane ne kamar kowa. Da aka tambaye ta kuma maganar aure sai jarumar ta fada cikin raha cewar ita duk wanda ma ya amince zai aure ta to a shirye take tayi masa lefe kyauta.
No comments:
Post a Comment