Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara
Mummunan gobarar ta kone shaguna a kalla 63 a kasuwar Tudun Wada da ke Gusau
- Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ziyarci kasuwar inda ya jajantawa musu kan afkuwa ifti'la'in
- Gwamnan ya kuma yi alkawarin sake gina shaguna da suka kone tare da bawa yan kasuwar tallafi Gobara a ranar Lahadi ta kone a kalla shaguna 63 a kasuwar Tundun Wada da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An kyautata zaton wutan ta taso ne daga wani shagon siyar da kifi wutar shagon ke da tangarda.
Yayin ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya jajantawa wadanda abin ya shafa ya ce su dauki abin a matsayin kaddara ne daga Allah.
Ya shawarci yan kasuwan su rika duba kayayyakin wutan lankarkinsu kafin su rufe shagunansu idan sun kammala ciniki na kowanne rana.
Ya ce gwamnatin jihar za ta sake gina shagunan 63 da wutan ya shafa kuma ya umurci kantoman riko na karamar hukumar Gusau ya fara aiki nan ba da jimawa ba.
Gwamna Matawalle ya kafa kwamiti karkashin jagorancin malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Umar Kanoma domin bincika irin asarar da yan kasuwan suka yi ya bada rahoto cikin kwanaki bakawai domin gwamnatin jihar ta san irin tallafin da za ta yi wa yan kasuwan. Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da taimakawa yan kasuwa da sauran masu treda domin habbaka tattalin arzikin jihar.

No comments:
Post a Comment