Friday, February 12, 2021

Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

 





Diyar biloniyan nan na Maiduguri, Rahama Indimi ta ce za a iya samun zaman lafiya bayan ma'aurata sun rabu - Ta yi wannan furucin ne a ranar Alhamis, tana tsaka da farin cikin samun babbar nasara akan Mohammed Babangida a kotu 


- A cewar Rahma, sau uku tsohon mijinta yana kai ta kotu don ya samu ya amshi yaransu, sai dai kuma ko yaushe nasara take samu Diyar wannan biloniyan na Maiduguri, Rahma Indimi ta ce akwai yuwuwar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakanin ma'aurata bayan sun rabu


Matar mai yara 4 ta bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan kwana biyu da samun nasararta a kotu, Shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

 A cewar Rahma, sai da tsohon mijinta, Mohammad Babangida, ya maka ta kotu har sau uku don ya samu a bashi damar rike su, amma ita take ta nasara. 



Tsohon mijina ya kai ni kotu don a bashi damar rike yaranmu, amma na yi nasara. 

Alhamdulillah. Karo na uku kenan," kamar yadda ta bai wa wani amsa da ya tambayeta a kafar sada zumunta ta Instagram. 

A shafinta ta bayyana wani tsokaci da tayi a Instagram, inda tayi godiya mara misaltuwa ga wadanda suka ba ta goyon baya. 

Ta shawarci zawarawa da su dinga maka tsofaffin mazajensu a kotu don su amshi yaransu. "Nagode sosai. Nagode da kwarin guiwar da ku ka bani. Ya kamata mutane su gane cewa ana samun natsuwa bayan rabuwar aure. Ba komai bane na fada. Tabbas idan ka sake aure, za a yi ta yada maganganu iri-iri." 


No comments:

Post a Comment

Pages