Yanzu Yanzu: SSG na Neja ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga
SSG na jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya jagoranci tawaga don ganawa da 'yan bindiga
- Matani ya bukaci yan ta'addan da su rungumi shirin yin sulhu domin samun maslaha ga lamarin rashin tsaro da ke addabar jihar
- Ya kuma nemi su ba gwamnati hadin kai a kokari da take yi don ceto matafiya da daliban makarantar Kagara da aka yi garkuwa da su a jihar Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya yi kira ga 'yan bindiga da su rungumi tattaunawa, sulhu sannan kuma su ajiye makamansu.
Sakataren jihar wanda ya raka malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi don ganawa da 'yan fashin ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta tattauna da su.
Kamar dai yadda 'yan fashin suka ba da sharadin zama lafiya a jihar sun ce akwai bukatar gwamnati ta saki mutanensu da ke hannun jami'an tsaro.
Matane ya yi jawabi ga ‘yan fashin da kwamandojinsu a Dutsen Magaji, karamar hukumar Mariga ta jihar Neja inda ya bukace su da su rungumi tattaunawar zaman lafiya da gwamnati ta fara. Ya bayyana cewa tattaunawar zaman lafiyar za ta kawo karshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, jaridar The Nation ta ruwaito. Matane ya kara yin kira ga Kwamandojin ‘yan fashin da su goyi bayan kokarin da gwamnati ke yi na ganin an saki fasinjojin da suka sace na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja da Daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara. Ya ce za a shigo da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki cikin tattaunawar da ake yi da ‘yan fashi, masu satar mutane, da barayin shanu a shirin samar da zaman lafiya da gwamnati ta fara.

No comments:
Post a Comment