Rikicin addini a Gombe: An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri
- Rikici ya barke a wani yankin jihar Gombe sakamakon rashin sanar sabon sarkin Tangale
- Rikicin ya haifar kona wuraren ibada tare da shagunan wasu al'umomin yankin da ma baki
- Gwamnan jihar ya sanya dokar hana fita a yankin zuwa wani lokacin da ba a sanar da budewa ba Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri. Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri.
Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu.
Kafin a a sanar da wanda gwamnan jihar ya zaba, wasu daga cikin mazauna yankin suka fara zanga-zangar nuna su dole a nada musu zabinsu; wanda daga bisani ya jawo tashin hankalin da ya kai ga tsare hanyar Gombe zuwa Adamawa tare kone-konen masallatai da shaguna.
Gwaman jihar ta Gombe ta fito yayi bayanin halin da ake ciki tare da bayyana matakin da ya dauka dangane da lamarin. Yake cewa: "Ya ku 'yan uwana, duk kuna sane cewa bayan rasuwar Mai Martaba, marigayi Abdu Buba Maisheru II, kuma daidai da dokokin da al'adun da muka shimfida, mun sanya ayyukan zabar sabon Mai Tangle," in ji shi.
. “Tsarin, wanda ya kasance a bayyane kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya haifar da tura mutane uku da aka ba da shawara ta hanyar sarakunan gargajiya na Tangale, daga cikinsu zan zabi dan takarar da zai cike kujerar Mai Tangle kamar yadda doka ta tanada.
" Gwamnan ya ce batun maye gurbin wani al'amari ne na Tangale tare da jihar Gombe kuma dukkanin wadannan mutane ukun da aka ba da shawarar sun cancanci sarautar Tangale ne saboda nasabarsu da masarautar Mai Tangale.

No comments:
Post a Comment