Wato Jama’ar Najeriya da dama suna tunanin Hanan Buhari itace diyar Shugaba Buhari ta karshe last Born, ashe abin ba haka yake ba.
NOOR (Amina Buhari) An haifeta A Shekara ta 2004, a ranar Sha hudu 14 ga watan Satumba lokacin mulkin Obasonjo, yanzu tana da shekaru 16 a Duniya.
Binciken M Inuwa MH ya tabbatar da cewa ita Noor Amina Buhari ba’a cika bayyana fuskarta ba sai sunanta shiyasa jama’a da dama basu santa ba sai na kusa kusa da Shugaba Buhari ne suka San asalin fuskarta.
Noor Amina Buhari ko a hoton family ba’a cika saka ta ba koma an sakata basu so su ambaci sunanta sakamakon ana so a boye ta.
Haka zalika account dinta na shafukan sada zumunta a kulle suke ba’a barin kowa ya shiga sai wanda ita Noor din taso ya shiga ma’ana private account ne.
https://hausapost.com/noor-amina-buhari-yar-autar-shugaban-kasa-buhari-da-kowa-baisanta-ba/




No comments:
Post a Comment